Saturday, August 29, 2009

Yadda Mutuwa Ta Yi Dirar Mikiya A Gidan Marubuciya Lubabah

Mutuwa da ake yiwa lakabi da riga ce ba ta fita ga kowa. Wata babbar aya ce daga mahaliccin kowa da komai da ya ke saukar da ita ga wanda Ya so, a lokacin da Ya so, ba kuma tare da shawartar mutum ba, walau da ciwo ko ba ciwo a tafi. Aba ce mai radadi, mai firgitarwa, mai jefa zukatan bayi cikin yanayin alhini da matsananciyar dawuwa. Kana kuma ma'abociyar yanke kiyayya ko kauna. Kamar yadda ta yanke igiyar kaunar da ke tsakanin marubuci Ibrashim Sheme da matarsa marubiya Binta Salma Muhammad. Kazalika yadda ta kawo karshen soyayya tsakanin marubuci Yaron Malam da ahalinsa. Kana kuma kamar yadda ta raba marubuciya Sadiya Garba Yakasai da danta.


Kansakalin na mutuwa ya zama Sila tare da datse igiyar soyayyar marubuciya Lubabah da 'yarta Rukayya Adamu (Murfat), ba da dadewa ba, ta dawo tare da kara karbar ran wani daga cikin 'ya'yan na ta Dawud Adamu (Anis). Bata kammala warwarewa daga matsanancin alhinin rabuwa da su ba, sai mutuwar ta sake kwankwasa mata kofa. Yaya Kenan? Wannan karon ma ran wani dan nata ta kara daukewa Hamisu Adamu (Abba). Da ace marubuciyar Ilham na da ikon hana mutuwa kara kwankwasa kofar gidanta, da ko shakka babu babu abinda da baza ta iya yi domin yin katangar karfe tsakaninta da ita ba. Duk da so shu'umi ne, mutuwar sai da ta yanke wanda ke tsakanin Lubabah da mijinta Ado Dauda Bichi.


Da ba don zurfafa imani da kaddara ba, ba mamaki batan basira ya sanya Lubabah ta yi zargin wani abu. Amma sanin cewar, wanda ya daka ta bado shi ruwa ya kan ci, sai ta dau halin girma, tare da fauwala komai ga wanda ya busa musu numfashin. Ta kuma kudire a ranta cewar, Kema haka zata iya faruwa a gareki. Bayan farfadowa daga halin zulumi da alhini gami kewar da ta kasance, a halin yanzu ta bankade labulen da ya yi mata shamaki da dakatar da rubutu da tayi a baya. Ta sake sakin wani sabon littafi sabanin tsintacciyar Mage, wanda ya ce namiji uba da kishin balbal. Maje El-Hajeej Hotoro ya ziyarci Lubabah, tare da tattaunawa da ita kamar haka:


A kwanakin baya kin rasa uku daga cikin 'ya'yanki ko za ki bayyana mana yadda abin ya faru?


Hakika na rasa yarana uku kusan lokaci guda, wanda wannan wani hukunci ne na ubangiji ne da ya kan jarabci bawa a duk lokacin da Ya so. Kuma wani hukunci ne da Shi Ya fi kowa sanin dalilin hakan.


Ko lokaci guda suka rasu?


Ba lokaci guda suka rasu ba. Tsakanin daya da daya kwana 42 ne, daya kuma shekara daya da wata shida.


Silar rasuwarsu fa?


Rukayya Adamu (Murfat) ta dan yi hadari ne. Dawud Adamu (Anis) rashin lafiya ya yi na kusan tsawon kwana shida, harma ya warware Allah Ya karbi abin Sa. Shi kuma Hamisu Adamu (Abba) heater ya taba ta dafa ruwan zafi, hakan ya zama sanadiyyar Allah Ya karbi abin Sa.


Bayan wadannan daga baya ma kin kara rasa maigidanki Ado Dauda Bichi. Ko yaya kika samu kanki?


Wannan duk cikin hukunci ne na ubangiji wanda Ya shirya duk wannan daki-daki.


Yaya zaki iya bayyana yanayin da kika kasance?


Gaskiya na shiga tashin hankali, na kuma dimauta da wannan al'amari. Amma imani da kaddara ya sani yiwa kaina fada. Domin a lokacin har na yankewa kaina kauna, gani na ke yi bazan kara samun wani farin ciki ba. Amma abune da Allah ne Ya ke dorawa bawa, kuma Shi Ya san yadda zai fitar da shi. Ban kuma san wane tanadi Allah Ya Yi min a gaba ba.


Ko hakan ya shafi harkar rubutunki?


Gaskiya ya shafa. Saboda bayan faruwar hakan komai ya fice daga raina, sai kwanan nan ne ma na dan dawo harkar.


Kusan yawanci marubuta kan so rubuta labarin wani abu da ya faru akansu. Ko kin yi sha'awar mayar da wannan abu da ya faru a gareki zuwa littafi?


Gaskiya ban yi sha'awa ba.


Dalili?


Saboda ban taba daukar wani abu da ya shafi rayuwata na mayar da shi littafi ba. Duk da dai cewar ya kamata a rubuta hakan domin nunawa mutane muhimmancin hakuri, yadda Allah Ya kan jarrabi bawansa da sauransu, amma ban yi sha'awar mayar da shi littafi ba.


Ko yaya zaki bayyana rayuwarki a halin yanzu?


Na san dole ka riga ka yi aure, ka zauna da mijinka amma yau babu shi, wataran zaka zauna ka yi tunani ko wani abu haka. Amma a halin yanzu ina cikin kwanciyar hankali babu kuma wata damuwa a tare da ni.


Kin ci gaba da rubutu kenan?


Yanzu ma na ci gaba da rubutu, domin na fitar da sabon littafi.


Sunansa?


Labule.


No comments: