Tuesday, October 20, 2009

Kisan gilla, Fyade, Ta'addanci da Keta Haddin Bil'adama A Kasar Guinea

Dubban 'yan zanga zangar kafin a bude musu wuta

Wani jami'in soji na yiwa mata mace daga cikin 'yan nzanga zangar zigidir.


A yayin da dimokradiyya ke dada samun gindin zama wasu kasashen duniya, a gefe guda kuma kasashen Afirka na tsaka da fuskantar babbar barazanar mulkin kama-karya, keta haddi, rashin 'yancin fadin albarkacin baki, murdiyar zabe da kuma uwa-uba mulkin mulukiyyya, ta hanyar muradin kasancewa a bisa karagar mulki ta ko wane hali. Kamar kwatankwacin yadda a halin yanzu shugaban kasar Nijar Tandhja Mammadu ya daura damarar wanzuwa a gadon mulki duk kuwa da bakar adawa gami da caccakar da 'yan kasar suke yi, tare kuma da kungiyoyin kare hakkin bil'Aama na duniya suka yi. Hakan bai hana shi sa kafa tare da tatsile kundin ntsarin mulkin kasar ba, don ya kai ga biyan bukatarsa. Ko a kwanan nan kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa na tuhumar shugaban kasar Sudan Al-Bashir da laifin kisan kiyashi ga 'yan kasar.
A yayin kasar Ghana ke bugun kirjin kafa tarihin gudanar da tsarkakakken zaben da ya rabauta da magudi, murdiya gami da yin amfani da karfin jami'an tsaro wajen gallazawa 'yan adawa. A Nijeriya da ake yiwa lakabida taurauwar Afirka ta kasa kai bantenta wajen yin karan tsaye ga kundin tsarin mulkin kasa, gami da keta hakkin bil Adama. Misali na karshe karshe shine yadda tsohon shugaban Nijeriya Obasanjo ya kakabawa 'yan kasar shugaba 'Yar Adua da karfin mulkinsaTa hanyar gurbataccen zabe mafi muni da aka taba gudanarwa a kasar kamar yadda wakilian sanya ido na kasa da kasa suka tabbatar.
Kazalika a ranar Litinin din 28 ga Satumbar 2009, dakarun sojin kasar Guinea suka yi luguden alburusai akan dubun dubatar 'yan kasar da suka gudanar da zanga zangar lumana a filin wasan tamaular dake babban birnin Conakry. Jami'an sojin sun yi galabar kashe adadin mutane 157, kana kuma lokaci guda suka raunata sama da 1, 253 nan take.
Silar zanga zangar kimanin mutane 50,000 din ta samo asali ne sakamakon, jita-jitar cewar, shugaban gardamammen sojan da yanke shine ke jagorantar akalar shugabancin kasar Capt Moussa Dadis Camara, wanda ya gaji kujerar a Disambar 2008, bayan mutuwar tsohon shugaban da ya fi kowa dadewa a mulkin kasar Lansana Conte, na da kudirin rikidewa domin tsayawa takara a zaben Janairun 2010. Wanda hakan wani sabon salon ci gaba da wanzuwa a bisa kujerar har sai yadda mansa ya kare. A yayin zanga zangar, jami'an soji sun yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa hasalallun, kana kuma lokaci guda suka rika dirka musu alburansan da ya zama sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama.

Yadda Soji Suka Ci Zarafin Mata Tare Da Yi Musu Fyade.
" Shekaruna 57, sun kuma yi min zigidir" Cewar wata mata, wacce fuskarta a sabule mako guda bayan faruwar lamarin. Lokacin da ta ke nunawa manema labarai kujejjen hannunta da kuma duwawunta. Ta kara da cewa, "Da idona na ga sojoji na sanya bindiga a matucin wata mata yayin da ni kuma suke dukana. Wani da ke dauke da wuka ne ya farde ilahirin kayan jikina. Sai na ce masa ni tamkar mahaifiya ce a gareka. Amma duk da haka sai da suka yanka na a duwawu da wukar, kana kuma ya lakada min dan karen duka." Baya ga ita, wata mata mai shekaru 47 mahaifiyar 'ya'ya biyu, ta nunawa manema labarai raunuka da kuma kukkujewa da ta yi a bayanta. " Wani soja ne ya daka ni tare da yi min tsirara. Ya dake ni a ka da bindigarsa. Suka yi ta dukana har sai da na fadi kasa. Sai wani ya zo tare da zura hannunsa a matucina, kana kuma suka yi min fyade. Zigidir haihuwar uwata na iyo tattaki daga wajen.
Thierno Maadjou Sow, Shine shugaban kungiyar kare hakkin bil Adama na kasar (Guinean Human Rights Organisation) ya kuma bayyana cewar, a halin yanzu suna hada kan matan da aka tozarta tare da yi musu fyade domin shigar da kara. Ya kuma jaddada cewar, sun wanzar da fyaden ne ido na ganin ido, wanda laifi ne da ya keta hakkin bil Adama.
Gawar wani daga cikin masu zanga zangar

Gwawwakin wasu matasa da aka kashe

Gawar wata da aka kashe

Dandazon gawawwakin masu zanga zangar

Wasu mutane dauke da gawa