Wednesday, September 2, 2009

Kisan Gillar Sheikh Ja’afar Mahmud Adam.

“ Wajibi ne akan shugaba ya tsare wa wadanda ya ke mulka rayuwar su, ta yadda za su iya barci har da munshari a gidajen su. Saboda samar da tsari na tsaro mai inganci, ta hanyar kare hannun duk wadanda aka san kai-ka-won su, zai iya zama barazana ga al’umma. Ta hanyar tabbatar da doka ga dukkan wanda ya ke yiwa dokar karantsaye.
Duk wanda ya firgitar da wani ko wasu ya hana su yin barci a kowane dalili, ko ta hanyar karbar dukiyar sa, ko a dalilin murdiya da jayayya, ko a dalilin kabilanci, ko wani dalili na daban. To ya kasance shugaba ya hukunta, wannan wanda ya hana wasu barci.”
Ko kadan marigayi Ja’afar Mahmud Adam, ba shi da masaniya a lokacin da yake futra wadannan lafuzza cewar, ‘yan sa’a’o’I kadan ne suka rage masa ya amsa kiran mahaliccin sa. Domin ya fade su ne a daren alhamis 12/04/2007 a yayin gabatar da taron wa’azi na musamman, da majalisar Ahlus-Sunnah ta shirya, domin yin bayanai akan ragowar babban zabe na musamman.
Kasancewar dawowar sa kenan daga jihar Bauchi, ya zo wajen a makare, don haka ya takaita batun sa, ko don cewa da ya yi duk yawanci abinda zai fada, ‘yan’uwansa sun fada. Kamar yadda ake yi masa a duk lokacin da ya halarci kowane majalisi, gabatar da sunan sa ke da wuya, gaba daya wajen ya dau kabbarori. Kuma a cikin jawaban sa, ya tabo muhimman batutuwa da suka shafi hakkin shugaba akan talakawan sa, da kuma suma hakkin shugaba akan su. Kasancewar dama an shirya wa’azin ne bayan sallar Magariba zuwa Isha’I, ana kammalawa, aka umarce shi da ya jagoranci sallah.
Washe garin ranar da wannan abu ya faru, juma’ar da ta zamanto jajiberen gudanar da babban zabe, sai garin Kano ya tashi da mumunan labarin rasuwar wannan dan taliki. Labarin da dubun-dubatar al’umma suka dauka tamkar al’amara da ga farko, kafin daga karshe su tsinci kan su cikin yanayin da duk iay fassarar mai fassara, ba zai iya kwatanta kwatankwacin wannan abu da ya darsu a zukatan su ba.
Bawai rasuwar Ja’afar ce ta girgiza zukatan al’umma ba, domin suna da cikakken yakinin kowane mai rai mamaci ne, kuma ciki har da shi din. Amma yadda ya rasu din shine babban abin tashin hankali ga duk wanda ya samu labarin cewar, da sanyin asubar juma’ar 13 ga Afirilun 2007 ya na tsaka da jan limacin sallar asuba a masallacin sa na Anmuntada, wasu fandararru suka afka har cikin masallacin gami da dandana masa zakin mutuwa, ta hanyar bindige shi har lahira.
Kamar yadda ladanin masallacin ya bayyanawa manema labarai cewar:
“ Muna cikin sallah ni da nake bayan sa, sai na jiyo takun kafa alamun mutum na tahowa. Kuma na fuskanci shi kan sa Malam din ya ji takun kafar. Kawai sai wasu mutane kusan 4 suka shigo, gami da harbin sa Fau! A daidai kasan hammatar sa, sai kuma suka bude wuta a cikin masallacin. Shi kuwa Malam sai ya yi kalmar shahada, tare da fadin:
“ Inna Lillahi Wa Inna Ilaihir-Raji’un.”
“Wanda tun daga nan bai kara cewa komai ba.”
Shin ko ta wacce kafa suka shigo?
“ Ta kofar da shi Malam din ya ke shigowa suka shigo.”
Bayan shi Malam din ko akwai wanda suka kashe ko kuma raunana?
“ Akwai wani makaho da duk lokacin da aka bude masallacin shine ya ke fara shigowa, sun harbe shi a kafa. Sannan akwai wanda suka harba, wanda shima nan take ya rasu.”
Ba ka tunanin ko cikin wa’azin sa na jiya, ya taba wasu da ba su ji dadi ba, wanda hakan zai iya sawa su yi masa wannan abin?
“ Malam bai taba kowa bacikin wa’azin sa, ya dai yi wa’azi ga shugabanni su ji tsoron Allah.”
Haka shima wani matashi da ya halarci salla tare da Malam din yayin faruwar al’amarin ya shaidawa wakilin mu cewar,
“ Wani abin mamaki shine masallacin ba karamin cika ya ke yi ba da sallar Asuba, musamman ma ranar juma’a. Amma a ranar gaba daya sahu uku ne, kuma shi kan sa Malam din sai da ya makara, har ana tunanin yin sallah, sai gashi ya shigo. Kuma a duk lokacin da ya shigo, ya kan rufo wannan kofa ta shigowar sa, amma a ranar sai ya barta a bude.”
Fantsamuwar wannan labari ke da wuya, al’umma suka shiga cikin matsananncin rudu gami da firgicewa, musammam ma da ya ke wani abu makamancin irin wannan bai taba faruwa a tarihin birnin na Dabo ba. Cikin kankanin lokaci sai ga shi masallacin da abin ya faru ya dankare da jama’a kamar kasa. Mafi yawancin su matasa, wanda kowa ka kalla kuka kadai ya ke iya yi. Yayin da wasu ke ta tintubar juna domin neman sanin yadda al’amarin ya faru. Kana kuma masu salula ke ta faman buga waya domin sanar da ragowar ‘yan’uwa abinda ya faru.
Bakunan mutanen wajen ya rarrabu zuwa gida biyu, wasu na tunanin kisan na da alaka da addini, yayin da wasu kuma ke danganta hakan da siyasa. Wanda hakan ya sa kowa ya yi ta kawo hujjojin sa, gami da kokarin gamsar da abokin zancen sa. Ganin yadda hankulan al’umma suka tinzura ne, ya sa aka umarci mutane da akyi sahu za’a tayar da sallah. Wanda nan da nan akayi yi sahu tun daga cikin masallacin har zuwa inda ba’a zato. Can bayan wani lokaci ka ce a tafi filin Firamare ta [orayi saboda nan din yayi kadan.
Bayan jama’a sun yi ta tururuwar tafiya can ne, sai aka kara umartar su da su kara yin sahu. Nan ma sai bayan kowa ya yi sahu, sannan aka kara sanarwa an daga yin sallar sai bayan sallar juma’a. Wasu sun koma gida domin karya gama da kimtsawa su dawo, yayin da wsu ko alamar motsawa daga wajen ba sa yi. Wanda ana tsaka da wannan abu ne, sai ga mai girma gwamna Malam Ibrahim shekarau nan ya zo, masu tsaron sa na buda masa tirmutsutsun al’umma domin ya shiga cikin masallacin. Wanda hakan ya janyo ‘yar hatsaniya, sakamakon wani matashi da ya fusata, gami da kai cafka da nufin damkar gwamnan. Wanda hakan ya sa wajen ya yamutse, wasu suka rika kokarin a buda masa ya shiga, yayin da wasu suka rika yunkurin hana shi. Amma daga karshe dai ya samu ya shiga.
Al’amarin da ya janyo rudu tare da hayaniya. Domin kusan duk cincirindon jama’ar wajen babu wanda ya goyi bayan wannan yunkuri da wasu suka yi.
“ In banda ma jahilci, yaya za’a kashe babban malami kamar Ja’afar, ace wai gwamna ba zai zo ba?”
Mafi yawancin kalaman da suka rika fitowa daga bakin mutane kenan. Gani al’amarin na neman rincabewa duk kuwa da tsauraran matakan tsaro da aka tanadar a wajen ne, ya sa aka umarci wani malami, ya tattaro hankulan mutane ta hanyar rarrashi da kuma siyasa. Wanda ya fara da bayyana yadda al’amarin ya faru, cewar an harbi malam ne da alburusai guda 6, wanda hakan ya sanya gaba daya wajen daukar kuwwa, saboda tausaya gareshi. Ya bayyana matsanancin alhinin sa, tare da alkawrtwa mutane cewar jinin Malam ba zai tafi a banza ba. Domin ga mai girma gwamna a wajen , ga manyan alkalai da masu fada aji, sun amince cewa komai zasu yi, zasu yi domin bankado wadannan ‘yan ta’adda.
Kana kuma ya yi ta rokon mutane da cewar, su ji tsoron Allah, su guji fadin munanan kalamai ga kowa, ko zargin wani bangare, tare da daukar doka a hannu. Su jira har sai an yi bincike, tare da gano ko su wanene tukunna. Kana kuma ya ci gaba da bayyana musu cewar, a halin yanzu ba Malam ne abin tausayi ba, domin ya yi mutuwar shahada, irin ta Sayyidina Umar (R.T.A) wanda shima aka riske shi har masallaci aka kashe shi. Kalaman sa sun kwantarwa da mutane hankali, tare da samun waje suka zauna har zuwa sallar juma’a. Wanda tunda aka bude masallacin bai taba karbar bakuncin dan Aadam irin na wannan lokaci ba.
Hudubar da aka gabatar yayin sallar juma’ar, ta kara tinzura al’umma, lokaci guda kuma ta zamanto mai sanyaya zukatan su. Domin dauke ta ke da ni’imomi tare da fa’i’dojin da Malam din zai samu, sakamakon mutuwar shahada da ya yi. Wanda har ta kai mai hudubar na fadin, suna masu kishin ina ma ace, suma su rabauta da irin wannan falala.
Bayan an kammala sallar juma’a, sai kuma yi masa sallah wanda ya gagara, domin gungun al’ummar da suka taru a wajen. Bazai iyu a ajiye gawar a sanya ta a gaba, gami da sallatar takamar yadda ake yi ba, sakamakon jama’ar da suka dandazo a wajen. Sai da ta kai limamin ya hau bisa motar gawar, aka yi sallar a haka. Domin ko fito da gawar ba a yi ba, saboda gudun yadda al’umma ke doki tare da rububin taba gawar. An samu samu kusan sa’a guda da rabi ana ta faman hada mutane da Allah akan su bari a fito da gawar, domin a rufe ta, amma abin ya ci tura. Mutane ran su ya baci sosai har suna ta fadin:
“ Sai kace ba musulmai ba? Don Allah ku matsa!”
Cincirindon jama’ar dai kowa so yak e ya samu ace ya taba gawar kafin a sanya ta cikin rami, wanda said a kyard a jibin goshi aka samu dammar bizne shi. Mutane maza da matan da suka halarci jana’izar ba abu ne da mutum zai yi tunanin kididdigewa ba, ko kuma tunanin kamantawa da wani taro ba. Wannan dan talilki da iko shakka babu ya samu matsananciyar soyayya gami da addu’o’in alkhairi ga dinbim al’umma. Musammam ma domin kasancewar tsananin tasirin da yake dashi a zuka tan mutanen da suke dafifi domin sauraren wa’azin sa.
A yayin day a ke mika ta’aziyyar sa, Malam Shekarau ya bayyana mamacin a matsayin wani gurbi babba da aka bari mai kuma wuyar cikewa. Kana kumaya bayyana bakin cikin san a wannan ta’annati da aka yi masa, kana daga karshe ya yi alkawarin ba za’a daina bincike ba, har sai an gano wadanda suka aikata wannan ta’addanci.
Shima a nasa sakon ta’aziyya shugaban kasa Obasanjo ya la’anci wadanda suka aikata wannan abu, tare da bayyana kisan a matsayin abin da bai kamata ba. Kana shima ya bayyana cewar jami,an tsaro na nan bias yunkurin suna gano wadannan ‘yan ta’adda.
An haifi malam Ja’afar Mahmud Adam ne a garin Daura da ke jihar Katsina a shekarar 1960. Amma kafin rasuwar sa, ya na zaune a jihar Kano , kana kuma duk shekara ya na gabatar da tafsiri cikin watan azumi, a masallacin Indimi da ke jihar Maiduguri . Ya bar mata 2 tare kuma da ‘ya’ya 6, bugu da kari ya na ci gaba da karatun digirin a na uku a Sokoto. Kafin rasuwar sa, malami ne da baya shakkar fadin gaskiya komai dacin ta, kuma ko akan waye, musammam ma yayin da aya da hadisai suka biyo ta kan ka. Kaza lika ya kasance ma’abocin hikimar Magana da kuma zalakar fayyace al’amura daki-daki ta yadda mutum zai iya fahimta cikin sauki. Yak an taba kowane bangare na rayuwa, bama akan matasa da kuma yadda zasu amfani rayuwar su, ta hanyar neman ilimin addini da kuma na zamani. Mai kuma son fige gaskiya ga mahukunta akan suji tsoron Allah, su yi gaskiya cikin lamuran su, da kuma yadda zasu inganta tattalin arzikin kasa da kyautata rayuwar talakawa.
Wanda yak an yi tafiye-tafiye jihohi daban-daban, ya na mai isar da sakon Ubangiji. Ya kuma samu karbuwa fiye da kima, domin nahiyoyi da daman a amfanuwa na daga wa’azozin sa. Mutane da dama daga garuruwa daban-daban, sun ci gaba da bayyana ta’aziyyar su, gami da jimamain sun a wannan abu day a faru a gareshi. Kana kuma a halin yanzu an dauki sara duk inda kaje kaset din wa’azin sa ake sanyawa. Masu sayar da kasa-kasai kuma na nan sun duk ufa sun a masu cinikin ire-iren wa’azin sa, musammam ma wanda ya yi ranar alhamis’ wanda shine na karshe kafin da asuba, yan ta’addar su halaka shi.

Monday, August 31, 2009

Boko Haram: An Kashe Maciji Ba a Sare Kansa Ba



A halin yanzu wannan ce muhawara mafi zafi da ake tattaunawa a zauruka da dama na yanar gizo. Duk munin laifin mai laifi babu wanda yake da hurumin zartas da hukunci a kansa matukar ba kotu ba. Jami'an tsaro kan iya harbin mai laifi a yayin da ya kasance sun yi taho-mu-gama kana kuma ya kasance dauke da makamin da zai iya kaiwa ga sanadiyyar rayuwarsu. Kuama a wannan yanayi ma sai idan babu wata sauran dabarar harbinsa a wani waje da za a iya kama shi da ransa domin gurfanar da shi a gaban kotu.

A ranar Alhamis din makon da ya gabata ne jami'an 'yan sandan kasar nan suka gabatar da gawar jagoran kungiyar ga manema labarai. Inda jaridu da dama suka buga hotonsa kwance male-male cikin jini gami da munanan raunukan da suka fi kama da harbin bindiga. Wanda hakan ya janyo 'yan sanda suka yi baki biyu wajen bayyana sakamakon mutuwarsa.
Da farko sun hakkake an kashe shine a yayin da dakarun tsaro sun kashe shi a harbe -harbe yayin da ya ke kokarin tserewa. Amma washegari sai jami'an soji ta bakin kwamandar rundunar murkushe 'yan kungiyar Kanal Ben Ahanoto ya bayyanawa manema labarai cewar, yana da rai a lokacin da aka mika shi ga 'yan sandan jim kadan bayan sun kama shi. Face kawai dan rauni da ya ji a hannunsa, wanda kuma an yi masa magani.

Amma sai 'yan sandan suka kara sakin wani bayani ta harshen kwamishinan 'yan sanda na jihar Borno Christopher Dega, inda ya bayyana cewar, a yayin da Mr. Yusif ya ke ma~oyarsa an yi musayar wuta da dakarun tsaro, wanda a sakamakon haka ya samu raunuka. Bayan an kama shi, an mika shi hannunsu ya gaza kai bantensa. Lamarin da ministan harkokin 'yan sanda Ibrahim Lame ya bayyana rashin jin dadinsa a yayin da ake zantawa da shi a sashen Hausa na BBC. Inda ya ce ya so a samu Muhammad Yusif da rai a gurfanar da shi a gaban kotu domin amsa tambayoyi.

Amma kasancewar hoto baya karya sai ga kafafen yada labarai sun wallafa hotonsa a lokacin da yake da rai, kuma dakaru na zagaye da shi, jim kadan kafin harbe shi har lahira. A hoton an ga Mohammed Yusuf, Shugaban kungiyar Boko Haram, ga alama a lokacin da aka kama shi, kuma kafin a mika shi ga 'yan sandan Nijeriyar. Wanda hakan ya jaddada zargin kungiyoyin kare hakkin bil Adama na cewar, an yiwa shugaban kungiyar kisan gilla (extrajudicial) ko kuma kisan ba bisa tafarkin da ya dace ba (illegal).

Bugu da kari an kara samun faifan bidiyo na minti 5 da sakwan 43 da jami'an suke masa tambayoyi. Wanda hakan ya kara wargaje batun 'yan sanda na cewar, ya cika ne a hannunsu sakamakon jikkata da yayi. Domin hatta ciwon da yake hannunsa da aka tambaye shi, cewa yayi faduwa yayi. Wanda hakan ya tabbatar ba wani harbi ko daya a jikinsa. Saànin wancan hoton gawarsa da aka nunawa duniya.

Kazalika Alhaji Buji Foi tsohon kwamishinan harkokin addini na jihar da 'yan sanda suka harbe, domin zarginsa da ake yi da daukar nauyin 'yan kungiyar, shima hotonsa ya bayyana a wasu jaridu da ransa kafin an daure masa hannu ta baya a wajen jami'an soji kafin 'yan sanda su harbe shi. bayyanar wani hoton bidiyo na sakwanni 40, ya nuna yadda jami'an kwantar da tarzoma suka kawo shi mota kirar Toyota Hilux. Foi wanda ya ke sanye da doguwar farar riga, kafarsa da hannunsa duk daure da ankwa, suka tarwatse suka barshi shi kadai.

Katsam sai jin karar bindiga aka yi na tashi, alburusai na isa gareshi. Kwamishinan da harsasai 6 suka same shi bai fadi ba, har sai bayan na 10 ya same shi sannan ya fadi. A yayin da aka ci gaba da harbin an ji sautin "kashe shi" "Ba an ba da oda ba?" na zayyanuwa cikin hoton bidiyon.

Tsohon kwamishina 'yan sandan jihar Legas Alhaji Abubakar Tsav, ya bayyana a Makurdi cewar kisan madugun kungiyar wani alaye na ~oye sunan 'yan siyasa da jami'an tsaro da suka da sa hannu cikin lamarin. Ta hanyar gurfanar da shi a gaban kotu ne zai iya fayyace su wane ne ke daure masa gindi domin suma a gurfanar da su. Amma kashe shi da 'yan sanda suka yi, hanya ce ta rufe bakinsa domin samun wannan bayani. Wa ya sani ma ko da sa hannun wasu daga cikin jami'an tsaron? Akwai yiwuwar nan gaba su sake bayyana ta wata sigar, domin mutum kadai da zai iya warware zare da abawar dangane da kungiyar an dinke bakinsa ta hanyar kashe shi da suka yi.

Sakamakon kashe shi da aka yi bayan za a iya kai shi kotu ya bankada sirrin komai, zai iya bawa wadanda suka daure masa gindi su koma gefe suna yada jita-jita iri daban-daban domin karkatai da hankalin jama'a. Ba mamaki jami'an tsaro ne? 'yan siyasa? Sarakuna? Ko kuma miyagun 'yan jari hujja? A bisa kwadayinsu na son dauwama akan karagar mulki abadan. Don haka kowa kan iya bin kowacce irin hanya na ganin ya cika kazamin muradinsa. Wanda sanin kowa ne a kasar nan ba da yawan jama'a ake cin za~e ba, face yin amfani da mahaukatan kudade tare da hada baki da jami'an tsaro ayi magudi.

Babban abin tambaya anan shine wane ne ya ke da umarnin bayar da kishe mai laifi a bayan fage ba tare da izinin kotu ba? Wane ne ya bayar da izinin kashe Muhammad Yusif da kwamishina Buji Foi bayan sakamakon alamomi da suka bayyana za a iya gurfanar da su a gaban kowacce kotu suyi bayani? Shugaban kasa? Shugaban 'yan sanda na kasa? Kwamishinan 'yan sanda na jihar? Gwamnan jihar Ali Modu Sherrif ? Sarki? Ko kuma attajiran jihar? Yanzu tsohon kwamishina Foi da ake zargi bashi da hakkin da za a kai shi kotu ya kare kansa?


Wai ina taken shugaban kasarmu na bin tafarkin doka da oda? Ina kwarmaton ministar yada labarai Dora Akunyili na farfado da martabar kasarmu? Amma sai gashi a jawabinta na BBC's Network Africa programme, tana bayyana cewar, abu mafi muhimmanci tunda dai ana kawar da shi daga doron kasa shikenan. Amma ta mittsike hakkinsa na cancantar a gurfanar da shi a gaban kotu. Domin bin diddigi, tare da bankado masu daure masa gindi. Idan dora na ganin da yawun lauyoyi da kuma alkalan kasar nan ta fadi wannan batu.


A gefe guda kuma sai ga shugaban kungiyar lauyoyi na kasa Oluwarotimi Akeredolu ya soki lamirin kashe shi da aka yi. Inda ya bayyana cewar, ko da an kama mai laifi karara da laifi ya cancanci a gurfanar da shi a gaban kotu tukunna kafin akai ga zartas masa da hukunci. Wanda wannan wani hakki ne da kundin tsarin mulkin kasa ya tanadarwa kowane dan kasa. A matsayinmu na 'yan kasa muna da hakki mu san dalilin da ya sa, 'yan sanda suka zartas da wannan hukunci bayan ya sa~awa tanadin dokar kasa kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999.