Thursday, September 10, 2009

Wednesday, September 9, 2009

TALAUCI A CIKIN HOTUNA









































































































































KASASSABA KO NEMAN NA ABINCI?




Masu azancin magana sun ce kowa da kiwon da ya karbe shi wai makocin mai akuya ya sai kura. A yayin da wasu ke ta faman fadi-tashin neman aikin dogaro da kai dare da rana safe da yamma daga masana'antu zuwa ma'aikatun gwamnati. A kuma yayin da wasu suka nema har suka gaza tare da fauwala komai ga mai kowa da komai. A kuma yayin da wasu suka zabi zama 'yan bangar siyasa a matsayin rufawa kai asiri. A kuma yayin da wasu suka gwammace zuki-fesar a dandi. Malam Isa Yakubu kuwa gwammacewa yayi da zaman banza gwamma bin kogo ko rami domin ya zura hannun sa ya damko maciji. Duk kuwa da cewar hakan ba karamar kasada ba ce, domin matsanacin hatsabibancin da ke tattare da shu'umar halittar da kaidin ta ke da matukar tasiri mai tsoratarwa ga rayuwar bil'Adama.
Ganin yadda jama'a ke darewa a yayin da ya tinkare su, dauke da shi a kafada ko kuma rike da shi a hannun kamar yana dauke da buhun masu gudan rana. Ya sa wakilin mu Maje El-Hajeej Hotoro tattaunawa da shi, musamman ma ganin yadda ya ke cunkusa kan macijin cikin bakin sa ya na tsotsa tamkar ya na mai tsotsar alwar dinya.
Ko yaya sunan Malamin?
Isa Yakubu.
Daga ina kenan?
Bauchi.
Ko wannan wasa da maciji da ka ke yi gado ne?
Gada na yi. Maciji ko wanne iri ne, ko na iska ne na riga shi na ce Allah. Ya Allahu ta rike bakin sa. Ni na ke danna hannu a kogo kowane iri ne zan janyo shi don na zagaya na gaida 'ya'yan sunnah.
Ko akwai wani magani da ka ke amfani da shi?
Wannan gado ne daga mahaifi zuwa kaka. Na taso daga gida na ga ana yin sa.
Kusan shekara nawa kenan ka na wannan sana'a?
Kusan shekara 34 kenan.
Ko ka taba haduwa da sharrin maciji?
Ina haduwa da macijin iska wanda ya ke cewa ya fi karfi na kuma da ikon Allah zan ci nasara akan sa kowane irin maciji ne. Maciji mai gemu, mai dan kuune, kowane iri ne ina yawan haduwa da shi a daji amma da yardar Allah ina kama su ba macijin da ya fi karfi na.
Ganin maciji na da sharri. Ko ka taba haduwa da sharrin sa?
Babu.
Da gaske kuma akwai na isaka kamar yadda wasu ke fada?
Sosai kuwa. Akwai mai gemu, akwai mai dan kunne, akwai kuma wanda zai yi maka magana ya ce ya fi karfin ka sai dai ka kama jikokin sa.
Ta yaya ku ke kama shi?
In dai za'a samu bakin abu a yanka, iskokin su bar kan sa, sai mu kama shi.
Ko da gaske ne idan mutum ya na cin maciji idan ya gan shi zai rika jin tsoron sa?
Kenan idan kana cin naman saniya idan ta gan ka sai ta gudu? Wannan duk fade ne kawai.
Da gaske ne maciji na jin magana?
Shi akwai jin magana domin har ya fi mutum jin magana.
Ko wanne shu'umanci ne ke tattare da maciji?
Akwai shu'umi kwarai kuwa.
Kamar yaya?
Akwai kwari. Za ka ganshi dan karami amma sai ya kumbura ya cika maka ido ya zama kamar tayar mota.
Ko jinsin macizai sun kai nawa?
Guda 100 ba 1 ne.
Lissafa mana kadan daga ciki?
Kasa, kububuwa, gansheka, jannasori, wuju-wuju, takwasara da sauran su.
Ko da gaske ne akwai macijin da ya ke tashi sama?
Sosai ma kuwa.
Kamar wadanne?
Akwai Darman, kububuwa, tsadaraki duk suna tashi sama.
Ina gaskiyar cewar kasa na shekara ta na barci?
Wannan duk fade ne idan ka zo kan ta za ta sa ni.



Monday, September 7, 2009