Ba mamaki zuwa yanzu babu sauran wanda zai kara kalubalantar haramcin ilimin boko. Wanda dama tsohon yayi ne da ya wanzu a arewancin kasar nan domin nuna kyamar mazauna yankin na ilimin boko a matsayin bokoko a wuta. Hakan kuwa ya samo asali ne kamar yadda masan tarihi suka bayyana sakamakon nuna adawa da turawan mulkin mallaka. Bayan malalar jinin daruruwan mutane sakamakon yamutsin da ya wanzu a wasu sassa na arewacin Nijeriya, ciki kuwa har da gogarman kungiyar masu adawa da ilimin bokon, zuwa yanzu kallo ya koma sama. A yayin da miliyoyin mutane a ciki da wajen kasar suka shiga dogon nazarin gano bakin zaren dalilan da ya sa aka kashe madugun kungiyar a bayan fage ba tare da an kai shi kotu an kalubalance shi ya kare kansa an kuma tabbatar an kama shi da hujja, sannan a kai ga yanke masa hukunci ba.
A halin yanzu wannan ce muhawara mafi zafi da ake tattaunawa a zauruka da dama na yanar gizo. Duk munin laifin mai laifi babu wanda yake da hurumin zartas da hukunci a kansa matukar ba kotu ba. Jami'an tsaro kan iya harbin mai laifi a yayin da ya kasance sun yi taho-mu-gama kana kuma ya kasance dauke da makamin da zai iya kaiwa ga sanadiyyar rayuwarsu. Kuama a wannan yanayi ma sai idan babu wata sauran dabarar harbinsa a wani waje da za a iya kama shi da ransa domin gurfanar da shi a gaban kotu.
A ranar Alhamis din makon da ya gabata ne jami'an 'yan sandan kasar nan suka gabatar da gawar jagoran kungiyar ga manema labarai. Inda jaridu da dama suka buga hotonsa kwance male-male cikin jini gami da munanan raunukan da suka fi kama da harbin bindiga. Wanda hakan ya janyo 'yan sanda suka yi baki biyu wajen bayyana sakamakon mutuwarsa.
Da farko sun hakkake an kashe shine a yayin da dakarun tsaro sun kashe shi a harbe -harbe yayin da ya ke kokarin tserewa. Amma washegari sai jami'an soji ta bakin kwamandar rundunar murkushe 'yan kungiyar Kanal Ben Ahanoto ya bayyanawa manema labarai cewar, yana da rai a lokacin da aka mika shi ga 'yan sandan jim kadan bayan sun kama shi. Face kawai dan rauni da ya ji a hannunsa, wanda kuma an yi masa magani.
Amma sai 'yan sandan suka kara sakin wani bayani ta harshen kwamishinan 'yan sanda na jihar Borno Christopher Dega, inda ya bayyana cewar, a yayin da Mr. Yusif ya ke ma~oyarsa an yi musayar wuta da dakarun tsaro, wanda a sakamakon haka ya samu raunuka. Bayan an kama shi, an mika shi hannunsu ya gaza kai bantensa. Lamarin da ministan harkokin 'yan sanda Ibrahim Lame ya bayyana rashin jin dadinsa a yayin da ake zantawa da shi a sashen Hausa na BBC. Inda ya ce ya so a samu Muhammad Yusif da rai a gurfanar da shi a gaban kotu domin amsa tambayoyi.
Amma kasancewar hoto baya karya sai ga kafafen yada labarai sun wallafa hotonsa a lokacin da yake da rai, kuma dakaru na zagaye da shi, jim kadan kafin harbe shi har lahira. A hoton an ga Mohammed Yusuf, Shugaban kungiyar Boko Haram, ga alama a lokacin da aka kama shi, kuma kafin a mika shi ga 'yan sandan Nijeriyar. Wanda hakan ya jaddada zargin kungiyoyin kare hakkin bil Adama na cewar, an yiwa shugaban kungiyar kisan gilla (extrajudicial) ko kuma kisan ba bisa tafarkin da ya dace ba (illegal).
Bugu da kari an kara samun faifan bidiyo na minti 5 da sakwan 43 da jami'an suke masa tambayoyi. Wanda hakan ya kara wargaje batun 'yan sanda na cewar, ya cika ne a hannunsu sakamakon jikkata da yayi. Domin hatta ciwon da yake hannunsa da aka tambaye shi, cewa yayi faduwa yayi. Wanda hakan ya tabbatar ba wani harbi ko daya a jikinsa. Saànin wancan hoton gawarsa da aka nunawa duniya.
Kazalika Alhaji Buji Foi tsohon kwamishinan harkokin addini na jihar da 'yan sanda suka harbe, domin zarginsa da ake yi da daukar nauyin 'yan kungiyar, shima hotonsa ya bayyana a wasu jaridu da ransa kafin an daure masa hannu ta baya a wajen jami'an soji kafin 'yan sanda su harbe shi. bayyanar wani hoton bidiyo na sakwanni 40, ya nuna yadda jami'an kwantar da tarzoma suka kawo shi mota kirar Toyota Hilux. Foi wanda ya ke sanye da doguwar farar riga, kafarsa da hannunsa duk daure da ankwa, suka tarwatse suka barshi shi kadai.
Katsam sai jin karar bindiga aka yi na tashi, alburusai na isa gareshi. Kwamishinan da harsasai 6 suka same shi bai fadi ba, har sai bayan na 10 ya same shi sannan ya fadi. A yayin da aka ci gaba da harbin an ji sautin "kashe shi" "Ba an ba da oda ba?" na zayyanuwa cikin hoton bidiyon.
Tsohon kwamishina 'yan sandan jihar Legas Alhaji Abubakar Tsav, ya bayyana a Makurdi cewar kisan madugun kungiyar wani alaye na ~oye sunan 'yan siyasa da jami'an tsaro da suka da sa hannu cikin lamarin. Ta hanyar gurfanar da shi a gaban kotu ne zai iya fayyace su wane ne ke daure masa gindi domin suma a gurfanar da su. Amma kashe shi da 'yan sanda suka yi, hanya ce ta rufe bakinsa domin samun wannan bayani. Wa ya sani ma ko da sa hannun wasu daga cikin jami'an tsaron? Akwai yiwuwar nan gaba su sake bayyana ta wata sigar, domin mutum kadai da zai iya warware zare da abawar dangane da kungiyar an dinke bakinsa ta hanyar kashe shi da suka yi.
Sakamakon kashe shi da aka yi bayan za a iya kai shi kotu ya bankada sirrin komai, zai iya bawa wadanda suka daure masa gindi su koma gefe suna yada jita-jita iri daban-daban domin karkatai da hankalin jama'a. Ba mamaki jami'an tsaro ne? 'yan siyasa? Sarakuna? Ko kuma miyagun 'yan jari hujja? A bisa kwadayinsu na son dauwama akan karagar mulki abadan. Don haka kowa kan iya bin kowacce irin hanya na ganin ya cika kazamin muradinsa. Wanda sanin kowa ne a kasar nan ba da yawan jama'a ake cin za~e ba, face yin amfani da mahaukatan kudade tare da hada baki da jami'an tsaro ayi magudi.
Babban abin tambaya anan shine wane ne ya ke da umarnin bayar da kishe mai laifi a bayan fage ba tare da izinin kotu ba? Wane ne ya bayar da izinin kashe Muhammad Yusif da kwamishina Buji Foi bayan sakamakon alamomi da suka bayyana za a iya gurfanar da su a gaban kowacce kotu suyi bayani? Shugaban kasa? Shugaban 'yan sanda na kasa? Kwamishinan 'yan sanda na jihar? Gwamnan jihar Ali Modu Sherrif ? Sarki? Ko kuma attajiran jihar? Yanzu tsohon kwamishina Foi da ake zargi bashi da hakkin da za a kai shi kotu ya kare kansa?
Wai ina taken shugaban kasarmu na bin tafarkin doka da oda? Ina kwarmaton ministar yada labarai Dora Akunyili na farfado da martabar kasarmu? Amma sai gashi a jawabinta na BBC's Network Africa programme, tana bayyana cewar, abu mafi muhimmanci tunda dai ana kawar da shi daga doron kasa shikenan. Amma ta mittsike hakkinsa na cancantar a gurfanar da shi a gaban kotu. Domin bin diddigi, tare da bankado masu daure masa gindi. Idan dora na ganin da yawun lauyoyi da kuma alkalan kasar nan ta fadi wannan batu.
/a>/>/>>/>
A gefe guda kuma sai ga shugaban kungiyar lauyoyi na kasa Oluwarotimi Akeredolu ya soki lamirin kashe shi da aka yi. Inda ya bayyana cewar, ko da an kama mai laifi karara da laifi ya cancanci a gurfanar da shi a gaban kotu tukunna kafin akai ga zartas masa da hukunci. Wanda wannan wani hakki ne da kundin tsarin mulkin kasa ya tanadarwa kowane dan kasa. A matsayinmu na 'yan kasa muna da hakki mu san dalilin da ya sa, 'yan sanda suka zartas da wannan hukunci bayan ya sa~awa tanadin dokar kasa kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999.
No comments:
Post a Comment