Saturday, August 29, 2009

Gidajen Rawa Tsirara A Kano?



Rawar na gudana ne a yayin da suke bin kidansu dake tashi wanda ake kadawa a wajen. Kuma matan na yin rawar ne sanye da shu'man tufafi ma'abota bayyanar da surorinsu. Kamar yadda wani da yake zuwa wajen ya tabbatar min, akwai yanayin wata rawa da matan ke yi da ake kira da turanci (Ass down) wani salo ne da matan kan janyo wandonsu kasa, domin bayyanar da wani sashi na duwawunsu, kana kuma daga gaba a samu damar ganin wani sashi na mararta.

A yayin da kida yayi kida matan na girgiza sassan jikinsu, su kuma mahalarta taron zasu rika kwarara ihu. Lokaci guda kuma suna farke bandir din kudi suna faman liki ba kakkautawa. Da dama daga cikin matan matasa ne kuma baligi farare kalkal, masu kyan diri da cikar halitta. Wanda dama Malam Bahaushe da aljanun son farar mace, ballantana kuma mutumin Kano! Wata majiyar ma ta tabbatar min da cewar, wani lokacin matan har sukan fayyace nonuwansu a zahiri. Ko kuma duwawunansu kacokam ga mutane.

Wani mahalarcin wajen ya shawarci wadanda basu fara zuwa wajen ba da su rufawa kansu asiri, domin a cewarsa, kallon rawar na da matukar nishadi. Kuma idan mutum ya fara, da wahala ya daina. Kuma irin wannan rawa ta samu karbuwa sosai a wajen matasa da kuma magidantan da sukan raba dare suna nishadantuwa da kallon tsiraicin fararen matan. Kana kuma matan na gabatar da kansu ga duk mai bukata matukar sun daidaita farashi. A church road, Enugu road da kuma Ecowas duk suna gudanar da wannan rawa. Kazalika suna yi sau biyu a otal din Royal Tropicana. Kamar yadda bincike ya tabbatar. Hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihara ita ce ke da alhakin kulawa da harkar kade-kade da wake-wake da kuma raye-raye, na kuma yi tattaki hukumar tare da ganawa da babban darakta Malam Rabo Abubakar.

A kwanakin baya wannan hukumar ta bayar sanarwa a kafafen yada labarai na tabbacin kama wasu mata na rawa tsirara a wani gidan rawa da ke unguwar Sabon Gari. Ina gaskiyar wannan batu?

Babu wani gida wararre guda daya da wanna hukuma ta taba bayar da sanarwa akansa. Gaskiya ne wannan hukuma tare da hadin gwiwar 'yan sanda da kuma kotu muna fita domin sa ido, wata fitar kuma dama muna da cikakken yakini na ana yin raye-rayen da suka sabawa shari'ah wadanda muke kira na batsa ko na badala. To a Sabon Gari irin wannan gidajen sun fi sau shurin masaki. Adadi mai yawa. Allah Ya banu iko mun yi aiki a kansu. Kuma 'yan jaridu sun dauki irin layin da suke so sun bada rahoto yadda suka fahimci lamarin.

Amma mu namu mu kama masu laifi babu cikin Sabon Gari, babu cikin gari babu wajen gari, lallai duk inda muka samu mai laifi zamu yi kokarin kamawa.

Rahotanni daga Sabon Gari sun tabbatar da akwai ire-iren wadannan gidaje da wasu 'yan kasar Chadi da Sudan ke rawa tsirara. Ko wannan rahoto ya zo muku?

Rahoto ko mutanen Nijeriya ne ko baki ne ya fi kama da hurumin wasu hukumomin. Raye-raye ko Baturen Ingila ne ya shigo cikin Kano, kasancewar an hana rawar batsa ba zamu kyale ba. Wannan rahoto shine ya ke bamu cikakken kwarin gwiwa na binciken da muka fara na wasu gidaje da har yanzu su akwai ragowar irin wannan rawa, suna fakewa da sunan na al'adarsu ne ko na gargajiyarsu ne. Kuma wannan abin da ya taso shi zai kara mana kaimi da hadin gwiwar jami'an tsaro musamman na farin kaya domin mu samu cikakken rahoto kafin mu kai garesu. Saboda na baya da muka yi, duk haka muka yi. Sai mun tara cikakkiyar hujja da bayanan da idan mun kai kara ba zamu fadi ba.

Zuwa yanzu ko kun rufe irin wannan gidajen sun kai nawa?

A kwaryar Sabon Gari gidajen raye-rayen batsa da na Disco da na Gala da na Mamin da na duk abinda za a iya tunani. Har na 'yan asharalle da sauransu akalla zasu kai gidaje 48.

A yayin da kake bayyana nasarorin wannan hukuma na rufe irin wadannan gidaje a Sabon Gari a kuma gefe guda hukumar Hisbah ta alakanta wannan aiki ga hurumin hukumar bude ido da shakawa ne wannan alhaki ya rataya a wuyansu. Ba ka ganin an kana keta huruminsu?

Hukumar Hisbah ina da tabbacin ta yi muku bayani ne a bisa abinda ta sani na doka don haka zai yi wuya tayi wani jawabi da zai yi karo. Kuma nima na yarda da Hukumar Hisbah rajista da tafiyar da al'amuran na gidan wasanni ko na shakatawa a karkashin hukumar Tourism yake. Amma mu inda muka shigo shine wanne irin abu ake yi a wajen shakatawar ko na bude idon? In anyi shi sabanin Shari'ah to muna da hurumi. Wannan ma ya sa komai kyan hajarka yayin kokarin sayar da ita, kai wani abu da ake kira badala ko wani sabo da ya keta dokokin wannan hukuma. Ba muna tuhumarka ya akayi ka samu rajistar sana'arka ba ne. Me ya sa aka same ka ka aikata ba daidai ba? Don haka muna da hurumi. Mu a fannin sa ido muke an yi daidai ko kuiwa a a, nan muke da hurumi.

Na garzaya ofishin hukumar shige da fice ta jihar inda na samu jami'in hulda da jama'a Nasiru Umar, wanda ya tabbatar min da wanzuwar wadannan mata. A zuwan farko na tarar sun kama wasu da tuni suka hankada keyarsu zuwa kasarsu. Yayin a zuwa na biyu nayi sa'ar samun wata matashiya mai suna Maryam, wacce ko ina na jikinta duk ta zane tatas da zanen furannin da ake kwalliya dasu na lalle a hannu da kafa. Na tambayi Maryam ko daga ina take ta ce daga jihar Maiduguri. Zancen da jam9i'in hulda da jama'ar ya nemi ta bashi lambar wayar mahaifi ko mahaifiyarta su kira indai sun tabbatar daga can ta ke zasu sake ta. Sai ta amsa da cewar, ta yar da wayarta. Da na tambayeta a ina suka kamo ta? Sai ta amsa da cewar church road. Me ake yi a wajen ta ce gidan rawa ne.

A binciken da na yi a wajen, na gano cewar, matan suna shigowa Nijeriya ne domin yin karuwanci. Domin akwai wacce ta bayar da tabbacin a kullum maza shida ne suke nemanta akan N500 kowane. Wanda hakan ya sa take samun jimlar N3,000 kullum. N90,000 a wata. A karo na uku ne da na koma nayi sa'ar an kamo su da dama. Inda har na shiga cikin ayarinsu a inda ake ajiye su kafin a mayar da su kasarsu. Farare ne sosai, wanda har wasu daga cikinsu na kara tasirin hasken nasu ta hanyar shafe-shafe. Daga cikinsu na tattauna da wata a takaice.

Yaya sunanki?

Zam zam.

Daga ina kike?

Chadi.

Ko kina da takardar izinin shigowa Nijeriya?

Babu.

Me ya kawo ki Nijeriya?

Yawo.

Sai dai ko kadan ban ga wani alamun damuwa tattare da su ba na kama su din da aka yi. Domin a bincikena na gano cewar da zarar an damka su ga hannun ofishin jakadancin kasar Chadi, sai su kara tsallakowa su dawo. Kuma na gano yadda wasu manyan masu fada aji na jihar ke karbarsu a hannun jami'an shige da ficen a duk sa'ad da suka kamo su. Domin ko a lokacin na samu tabbacin wani mai rawani da ya aike da katinsa na a saki wata daga ciki. Jami'in hulda da jama'ar ya koka matuka da wannan karuwanci da suke yi, domin kamar yadda ya fada akwai yiyuwar yaduwar miyagun cututtuka. A takaice ma har shaida min yayi cewar, ba irin rokon da basa yiwa matan su nemo mazan aure su kuma zasu barsu su zauna a kasar, idan barinta ne basa son yi.

Daga karshe na samu kididdigar hukumar tayi nasarar cafke adadin matan guda 16, daga watan Afirilun wannan shekarar zuwa lokacin hada wannan rahoto.

No comments: