Tuesday, August 25, 2009

Laifin Me Mazauna Darul Islam Suka Yi?


Ina fatattakar 'yan Darul-Islam da gwamnati tayi? Laifinsu kawai shine domin sun zabi kauracewa daga cikin mutane da suke ganin tarbiyya ta lalace sun zabi komawa wajen gari su gudanar da addininsu gwargwadon fahimtarsu? Fahimta fuska ce. Kuma kundin tsarin mulkin kasa yabawa kowa 'yancin zabin addini. Ko kadangare mutum ya ce zai bautawa yana da wannan hakkin. Duk binciken da aka gudanar ya nuna mutanen nan basu da alaka da kungiyar boko haram. Suna ma da makaranta a yankin dake koyar da karatun boko. An kuam saka koyarwa a sashin Hausa na BBC duniya taji, yayin da wakilinsu ya gudanar da bincike na musamman a garin.



Mutanen nan da kansu suka nemi hukuma ta kai rangadi tare da gudanar da duk binciken da ya dace. Daga gida zuwa gida aka rika bincike ba a same su da makamai ba. An tintubi makotansu sun bayar da shaidar mutane ne masu son zama lafiya. Babu kuma wani yamutsi da ya taba hada su da kowa, tsawon shekaru 17 da suka yi a wajen. Suna tsaka da sallar asubashi jami'an tsaro suka tattare su tare da kai su wata makaranta aka rika bincikensu na tsawon wani lokaci. A cewar wani shugabansu yayin da ake tattaunawa dashi ta wayar salula washegari, ya bayyana cewar, wajen da aka ajiye su, babu abinci, babu wajen kewayawa, babu cikakkiyar kulawa, ga yara kwance a kasa ba lafiya. Hakkin bil Adama kenan?


Ina tanadin dokar kasa sashi na 41 da ya bawa kowane dan kasa 'yancin walwala da yawatawa a kowane yankin na kasar? Babu wata doka daga cikin tsarin kundin mulkin 1999 da ya bayar da izinin kama mutum haka kawai don ya zabi zama a wani yankin Nijeriya matukar dan kasa ne. A sashi na 46 na kundin tsarin mulkin kasar nan ya hana a tashi dan kasa daga wani yanki da ya zabi zama, sai dai a kai shi kotu. Kuma ko da kotun ta nemi ya tashi daga wajen, sai an biya shi diyya. Mutanen nan manoma ne, sunyi shuka, basu girbe ba, an tarkata su, an mayar da su inda suka fito. Ba tare da umarnin kotu ba, ba tare da an biya su diyya ba. Ina hakkin bil Adama?


Hala gwamnati bata tunanin wannan wani sabon salon barna suka bude? Domin idan sun mayar dasu inda suke, me suka tanadar musu? Me zasu rika yi a can? Ba sa tunanin sauya musu tunani daga masoya zaman lafiya, zuwa masoya neman ramuwar gayya wacce tafi ta gayya zafi ko ba dade ka ba jima? Kuma ko ta wacce hanya? Ba sa tunanin nan gaba irin wadannan mutanen da aka gallazawa bama kungiyar boko haram ba, ko kungiyar ci da sha haram, aka gayyace su zasu iya mika wuya? Basa tunanin nan gaba kowane gwamna zai iya kafa hujja da wannan dalili a gaba ya kori duk bakin johohin mazauna jiharsa, musamman ma idan suka samu bambanci ra'ayin siyasa? Basa tunanin ire-iren dangogin wadannan take haddi ne, ya haifar da ambaliyar kunar bakin-wake da 'yan bindiga dadi da yau suka zamewa duniya alakakai?


1 comment:

Anonymous said...

Loved your site, Lee! Thanks for sharing Kami menyediakan berbagai macam obat seperti Obat kondiloma , Kencing Nanah , Wasir , Sipilis , Herpes , Diabetes